Najeriya-Kano

Dattawan Kano sun bayyana kaduwa da matakin tsige Sarki Sunusi

Tsohon Sarkin Kano mai martaba Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu.
Tsohon Sarkin Kano mai martaba Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu. Getty Images

Kungiyar dattawan Kano mai suna “Advocates For a United Kano” ta bayyana kaduwa gami da mamakin matakin gwamnatin jihar na tsige mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na 2 daga kan karaga.

Talla

A yau litinin 9 ga watan maris na 2020, sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ya bayyana matakin na tsige Sarki Sunusi na 2 bisa tuhumarsa da da wulakanta al’adun al’umma da kuma masarautar da yake jagoranta.

Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji kan tsige Sarki

Cikin sanarwar da suka fitar, dattawan na Kano karkashin jagorancin Alhaji Bashir Usman Tofa, sun bukaci daukacin al’ummar jihar da su kaucewa tayar da tashin hankali da sunan adawa da matakin tsige Sarkin, la’akari da cewa babu wanda ya san karshen fitina idan aka yi kuskuren tayar da ita.

Dattawan sun bayyan rungumar abinda ya faru a matsayin kaddara daga Allah mai kowa mai komai.

Daga karshe sanawar ta ce dattawan za su ci gaba da kalubalantar gwamnatin Kano ta fuskar shari’a kan dukkanin matakan da take dauka na ba dai dai ba, ciki kuwa harda dokar bada damar tsige Sarkin da majalisar dokokin jihar ta Kano ta kada kuri’ar amincewa da ita a wannan litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI