Gwamnatin Ganduje ta tsige Sarkin Kano daga karaga
Gwamnatin Kano da ke Najeriya ta tsige Sarkin Kano, Alhajji Muhammadu Sanusi na II daga karagarsa saboda rashin mutunta ofishin gwamna da sauran hukumomin gwamnatin jihar kamar yadda gwamnatin ta ce.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usaman Alhaji ya ce, tsigewar za ta fara aiki nan take .
Sakataren ya ce, ayyukan Sarkin sun saba wa kashi na 3, sashi na A-E na dokokin jihar Kano, abin da ya sa aka tsige shi.
A cewar sakataren, sun tuntubi masu ruwa da tsaki kafin daukar matakin tsige Sarki Sanusi, yana mai cewa, nan kusa za a sanar da sabon sarkin da zai gaji Sanusi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu