Najeriya-Kano

Gwamnatin Kano ta nada sabon Sarki

Sabon Sarkin Kano mai martaba Aminu Ado Bayero.
Sabon Sarkin Kano mai martaba Aminu Ado Bayero. Solacebase

Gwamnatin Kano ta nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin jihar bayan tsige tsohon Sarki Muhammadu Sunusi na 2.

Talla

Kafin nada shi kan mukamin, da ga tsohon Sarki marigayi Ado Bayero, Aminu Ado ne Sarkin Bichi, daya daga cikin sabbin Masarautu guda 4 da gwamnatin Kanon karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira cikin shekarar bara.

Cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin Kano ta hannun sakataren ta Alhaji Usman Alhaji, matakin zabar Aminu Ado Bayero a matsayin Sarki ya biyo bayan amincewar majalisar masu zabar Sarki a masarautar ta Kano.

Gwamnatin Kano ta tsige tsohon Sarki Muhammadu Sunusi na 2 ne bayan tuhumarsa da laifin wulakanta al’adun al’umma da kuma masarautar da ya jagoranta, gami da daraja gwamnatin.

An dai shafe tsawon lokaci ana takaddama tsakanin tsohon Sarkin da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, duk da cewa bangarori da dama sun yi kokarin sansanta su.

Bayan shafe kimanin shekaru 5 bisa mulki ne baraka ta soma kunno kai tsakaninsa da gwamnati, wadda da fari ta tuhume Sarki Sunusi da barnatar da miliyoyin kudin da aka ware domin amfanin masarautarsa.

Dangantaka ta cigaba da yin tsami tsakanin tsohon Sarkin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda cikin yanayin ne kuma aka kirkiri sabbin masarautu 4 masu daraja ta 1, da suka hada da Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya.

Tsohon Sarki Sunusi Lamido Sunusi ya ci gaba da yin tsokaci kan halin da kasa ke ciki, inda makon jiya ya zargi ‘yan siyasa, sarakunan gargajiya da kuma malaman addinin arewacin Najeriya da yin watsi da nauyin kulawa da yankin abinda ya haifar da babban gibi tsakaninsu da Kudancin kasar.

Har yanzu dai babu rahotannin samun tashin hankali a jihar Kano biyo bayan matakin tsige tsohon Sarkin, kamar yadda aka taba gani a shekarar 1963, lokacin da gwamnatin arewacin Najeriya a waccan lokacin ta tsige kakansa Sarki Sunusi daga Sarautar bijire mata.

Zalika a shekarar 1981 an taba fuskantar boren jama'a a lokacin da gwamnatin Kano ta dakatar da Sarkin waccan lokacin Marigayi mai marataba Alhaji Ado Bayero, matakin da ake zargin na shirin tsige shi ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI