Halin da aka shiga bayan tsige Sarki Sunusi
Gwamnatin Jihar Kano a Najeriya, a wannan litinin ta tsige mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu, bayan share dogon lokaci ana takaddama tsakanin Sarkin da kuma Gwamnati wadda ke zarginsa da wulakanta al’adun al’umma da kuma masarautar da yake jagoranta.Bayan sanarwar cire Mahammadu Sanusi na biyu daga wannan matsayi, nan take aka tura jami’an tsaro zuwa fadarsa, inda tuni aka fitar da Sarkin.Daga Kano, wakilinmu Abubakar Isah Dandago ya aiko mana da karin bayani dangane da halin da ake ciki.
Wallafawa ranar:
Halin da aka shiga bayan tsige Sarki Sunusi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu