Najeriya-Coronavirus

An samu mutum na 2 da ya kamu da cutar Coronavirus a Najeriya

Wani jami'in lafiya yayin nazari kan cutar Coronavirus.
Wani jami'in lafiya yayin nazari kan cutar Coronavirus. Wera Rodsawang/Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta sanar da samun mutumi na biyu da ya kamu da cutar coronavirus ko kuma COVID-19 a cikin kasar.

Talla

Hukumar yaki da cututtuka ta sanar da cewar an gano mutumin ne cikin wadanda suka yi mu’amala da dan kasar Italiar dake dauke da cutar a watan jiya a Jihar Ogun.

A ranar 28 ga watan jiya aka gano wani dan kasuwa daga Italia da ya shiga Najeriya dauke da cutar, ya kuma ziyarci birnin Lagos da Jihar Ogun.

Wannan ya sa hukumomin Najeriya killace mutumin da kuma mutanen da yayi mu’amala da su domin tantancewa.

Gwamnatin Najeriya tare da na Jihohin Lagos da Ogun sun bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankalin su domin suna daukar matakan da suka dace domin kare lafiyar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI