Najeriya

Budurwa ta kashe wanda ya yi yunkurin yi mata fyade

'Yan sandan Najeriya a fagen aiki
'Yan sandan Najeriya a fagen aiki Premium Times Nigeria

Wata budurwa ta kashe wani mutum da ya yi yunkurin yi mata fyade a yankin Iyana Kpaja da ke Lagos a Najeriya.

Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Lagos, Bala Elkana, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce mutumin da aka kashe, Babatunde Ishola, mai shekaru 49 mai gadi ne a makarantar sakandare ta Ogoru High School da ke yankin na Iyana Kpaja.

Budurwar da ba bayyana sunanta ba, ‘yar shekarar 16 ce da ke ajin karshe a makarantar sakandare, kuma take unguwar Ogundele Street a Iyana Kpaja.

Sanarwar da ‘yan sanda suka fitar ta ce yarinyar ta je gidan mamacin ne don ta taimaka mai wajen dibar ruwa a ranar Asabar, duba da cewa hi kadai yake rayuwa.

Marigayi Ishola dai aboki ne ga mahaifin wacce ake zargi da kashe shi, kuma ta saba taimaka mai da ayyuka a gida.

Bala Elkana ya ce yayin da budurwar ke kokarin taimaka mai da ayyukan da ta saba ne ya nemi ya yi lalata da ita, hakan ya sa ta dauki wuka ta daba mai.

Kakain ya ce ‘yan sanda sun je har gidan, inda suka tarar da mamacin kwance cikin jininsa.

Yanzu dai an kai gawar mamacin asibiti, ita kuwa budurwa tana tsare a ofishin ‘yan sanda har sai an gama bincike kamar yadda kakain ‘yan sandan Lagos din ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.