Najeriya-Kaduna

Gwamnan Kaduna ya baiwa tsohon Sarkin Kano mukami

Gwamnatin jihar Kaduna dake Najeriya ta nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II a matsayin mataimakin shugaban majalisar gudanarwar hukumar zuba jari ta Jihar kwana guda bayan tube shi daga Sarautar Kano.

Tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu tare da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai.
Tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu tare da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai. Pulse Nigeria
Talla

Gwamnan Jiahr Malam Nasir El Rufai ya sanar da nada shugabannin hukumar a karkashin jagorancin mataimakiyar Gwamnan Jihar Dr Hadiza Balarabe domin ganin sun taimaka wajen janyo hankalin masu zuba jari zuwa jihar.

El Rufai ya bayyana fatar sa na ganin Jihar Kaduna ta mafana daga ilimi da kwarewar Sarkin da kuma irin mutanen da ya sani a kasashen duniya.

Gwamnan ya yabawa wakilan kwamitin gudanarwar saboda amincewa su yiwa jihar aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI