Najeriya-Kano

Gwamnatin Nasarawa ta sauyawa tsohon Sarkin Kano masauki

Tsohon Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu bayan isa jihar Nasarawa.
Tsohon Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu bayan isa jihar Nasarawa. Daily Trust

Rahotanni daga Nasarawa a Najeriya, sun ce gwamnatin jihar ta sauyawa tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na 2 masaukin da ta soma bashi a kauyen Loko dake karamar hukumar Nasarawa, zuwa karamar hukumar Awe.

Talla

Jaridar Daily Trust dake Najeriya ta ruwaito cewar an sauyawa tsohon Sarki na Kano masaukin ne saboda dalilai na tsaro da kuma walwala.

A ranar litinin 9 ga watan Maris na 2020 gwamnatin Kano ta tsige Sarki Sunusi bayan tuhumarsa da rashin mutunta gwamnatin jihar, da wulakanta al’adun al’umma da kuma masarautar da yake jagoranta, zargin da a baya ya sha musantawa.

Wata majiya data nemi a sakaya ta, ta ce da fari an shirya maida tsohon Sarkin na Kano ne zuwa garin Opanda dake karamar hukumar Toto, sai dai daga bisani aka janye kudurin saboda sanya bakin wasu dattijai, da suka hada da Mai Martaba Sarkin Lafia mai Shari’a Sidi Bage, Janar Aliyu Gusau da kuma Hamshakin attajirin nahiyar Afrika Aliko Dangote.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI