Najeriya ta dakatar da gasar kwallon kafa saboda mutuwar dan wasa
Wallafawa ranar:
Hukumar kwallon kafar Najeriya ta sanar da dakatar da gasar kwallon kwararru da ake gudanarwa a kasar sakamakon mutuwar dan wasan kungiyar Nasarawa United Chieme Martins a karshen makon da ya gabata.
Hukumar ta bukaci daukacin kungiyoyin kwararrun da su samar da kayan kula da lafiya a kowanne filin wasa domin kare lafiyar jama’a.
Mai magana da yawun hukumar yace binciken da suka gudanar ya nuna musu cewar rashin kayan kula da lafiya da kuma jami’an lafiya ya taimaka wajen asarar ran ‘dan wasan a karawar da akayi tsakanin Nasarawa United da Katsina United.
Hukumar kwallon bata yi bayani kan lokacin da za’a koma cigaba da wasannin ba, wanda ya zuwa yanzu kungiyar Plateau United ke matsayi na farko da maki 43 bayan wasanni 23.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu