Najeriya-Kano

Tsohon Sarki zai kalubanci matakin fitar da shi daga Kano

Tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi na 2, ya sha alwashin garzayawa kotu, domin kalubalantar matakin fitar da shi daga jihar ta Kano zuwa wani wuri da nufin zama sabon mazauninsa.

Tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sunusi Lamido Sanusi na 2.
Tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sunusi Lamido Sanusi na 2. AFP
Talla

Tsohon Sarkin ya bayyana haka ne ta hannun lauyansa Abubakar Balarabe Mahmood mai darajar SAN a ranar talata 10 ga watan Maris, yayin taron manema labarai birnin Kano.

Mahmood ya ce babu wanda ya mikawa tsohon Sarkin takardar sammaci a lokacin da jami’an tsaro suka fitar da shi daga fada a ranar litinin da ta gabata, jim kadan bayan sauke shi daga mulki.

Lauyan yace matakin majalisar kolin gwamnatin Kano na fitar da tsohon Sarkin daga jihar ya sabawa doka, dan haka matakin ya tauyewa mai Martaba Sunusi Lamido Sunusi na 2 hakkinsa na dan adam.

Ranar litinin 9 ga watan Maris na 2020 gwamnatin Kano ta tsige Sarki Sunusi bayan tuhumarsa da rashin mutunta gwamnatin jihar, da wulakanta al’adun al’umma da kuma masarautar da yake jagoranta, zargin da a baya ya sha musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI