Al'ummar Kaduna sun koka kan rusa kasuwar barci

Sauti 09:57
Kasuwar Barci dake birnin Kaduna
Kasuwar Barci dake birnin Kaduna RFI Hausa

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannnan mako tare da Ahmed Abba, ya maida hankali ne kan matakin gwamnatin jihar kaduna dake Najeriya na rusa kasuwar barci dake jihar a kokarin sake fasalin zamanantar da kasuwanni birnin Kaduna daga yadda suke, matakin da ya tada hankalin 'yan kasuwa da al'ummar birnin.