Najeriya

Ba mu fitar da Sanusi daga Kano ba- Gwamnatin Ganduje

Sanusi Lamido Sanusi bayan ya fice daga Kano jim kadan da warware masa rawani
Sanusi Lamido Sanusi bayan ya fice daga Kano jim kadan da warware masa rawani Daily Trust

Gwamnatin Kano da ke Najeriya ta ce, babu hannunta a tasa keyar tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II zuwa jihar Nasarawa da kuma tsare shi ko hana shi walwala kamar yadda doka ta ba shi dama.

Talla

Kwamishinan Shari’ar jihar, Barr. Ibrahim Mukhtar ya bayyana haka a zantawarsa da RFI Hausa, yana mai cewa, gwamnatin ta sauke Sanusi ne kawai daga kujerarsa amma ba ta da hannu game da fitar da shi daga jihar Kano.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanan Barr. Mukhtar.

Ba mu fitar da Sanusi daga Kano ba- Gwamnatin Ganduje

Barr Mukhtar ya ce, jami’an tsaro ne suka yanke shawarar tasa keyar Sanusi daga Kano saboda wasu bayanan sirri da suka samu.

Kwamishinan ya kara da cewa, fitar da sarki zuwa can wani wuri, ta zama tamkar al’ada domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A bangare guda, shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya ce, ba shi da hannu ta kowacce hanya kan tsige Sanusi daga karagar Masarautar Kano.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mai Magana da yawun Buhari, Garba Shehu ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa, da hannun shugaban kasar a cikn wannan al’amari, yana mai cewa, an shigar da siya cikin batun tsige Sanusi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.