Najeriya

Mutumin da ya kamu da Coronavirus a Najeriya ya warke

Kasashen Afrika na daukar matakan hana yaduwar Coronavirus
Kasashen Afrika na daukar matakan hana yaduwar Coronavirus REUTERS/Francis Kokoroko

Hukumomin Najeriya sun ce, mutum na biyu da ya kamu da cutar Coronavirus ya samu sauki kuma an gwada shi ba tare da samun cutar a jikinsa ba.

Talla

Ministan Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana haka, inda ya ce ya zuwa yanzu mutane biyu ne kawai aka tabbatar sun kamu da cutar da suka hada da ‘dan kasar Italiya da ya shiga kasar da ita da kuma ‘dan Najeriyar da ya yi mu’amala da shi.

Ehanire ya ce, yayin da shi dan kasar Italiya ke ci gaba da murmurewa, dan Najeriyar ya samu sauki kuma za a bar shi a gida.

Ministan ya ce, jami’an ma’aikatarsa za su ci gaba da sanya ido sosai kan masu shiga kasar domin dakile samun cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI