Najeriya

Dalilin da ya sa ba zan kalubalanci sauke ni ba - Sanusi

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai tare da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na 2.
Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai tare da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na 2. Daily Trust

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II yayi bayani kan dalilin da ya sa ba zai je kotu ba domin kalubalantar gwamnatin jihar Kano da ta sauke shi daga mukamin sa.

Talla

Sanusi yace yayi iya abinda zai iya yi a cikin shekaru 6 da suka gabata, saboda haka shi yanzu yana hararen gaba ne, kuma babu dalilin komawa baya.

Wani faifan bidiyo da aka nada ya ruwaito Sanusi na cewa, inda yana bukatar kalubalantar matakin zai yi nasara, domin wasikar da aka rubuta na sauke shi na dauke da kura kurai, kuma abu mai sauki ne yaje kotu.

Sanusi yace babu abin bakin ciki a gare shi, duk da yake matakin bai masa dadi ba, abinda ya faru ya faru.

Yayin da ya sauka a Lagos daren jiya Sanusi yaki cewa yan jaridu komai dangane da lamarin.

A wani labarin kuma,babban hadimin tsohon Sarkin Kano mai Martaba Sunusi Lamido Sunusi na 2, Alhaji Munir Sunusi Dam Buram, ya zargi ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami da kuma Kwamishinan shari’ar jihar Kano da bada umarnin tsare Sarkin a karamar hukumar Awe dake jihar Nasarawa, bayan sauke shi daga mulki.

Ranar 9 ga watan maris din nan ne dai Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zartas da matakin sauke tsohon sarkin bisa tuhumarsa da rashin mutunta gwamnati.

Rahotanni sun ce da fari Sarkin ya so tashi daga Kano zuwa Legas tare da iyalansa amma kwamishin ‘yan sandan jihar yace umarnin da aka bashi shi ne raka shi zuwa jihar Nasarawa, sai dai bai bayyan wadanda suka bada umarnin daga sama kamar yadda ya bayyana.

Ranar Juma’a ne kuma wata babbar kotu a Najeriya ta baiwa gwamnatin kasar umurnin gaggauta sakin tsohon Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi daga tsarewar da aka yi masa a garin na Awe.

A daren ranar ta Juma’a tsohon Sarkin ya sauka a jihar Legas tare da rakiyar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.