Najeriya

An kammala bikin kamun kifin Argungu

An kamala bikin kamun kifin Argungu a Najeriya da aka kwashe shekaru ba’ayi ba saboda matsalar tsaro, inda Abubakar Ya’u daga karamar hukumar Augie ya samun nasarar zaman a farko da kifi mai nauyin kilo 78.

Wasu daga cikin wadanda suka fafata a bikin gasar kamun kifin Argungu.
Wasu daga cikin wadanda suka fafata a bikin gasar kamun kifin Argungu. RFIHausa/Faruk Yabo
Talla

Wannan nasara da ya samu daga cikin masunta sama da 50,000 da suka shiga gasar ta sa ya samu kyautar naira miliyan 10 da motoci guda biyu da kuma kujerun Makkah guda 2.

Baka Yahaya Bagaye ya samu nasarar zaman a biyu da kifi mai nauyin kilo 75, sai kuma Sani Maiwake da ya zo na 3 da kifi mai nauyin kilo 70.

Rahotanni sun ce shugaban Gwamnonin Arewacin Najeriya, Simon Lalong ya bada kyuatar naira miliyan 3 ga wanda ya zo na farko, miliyan 2 ga wanda ya zo na biyu sai kuma miliyan guda ga wanda ya zo na 3, kamar yadda Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayar.

Babban Sakataren hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Najeriya Hassan Bello ya baiwa wanda ya zo na farko kyautar naira miliyan guda, na biyu naira 750,000 sai kuma wanda ya zo na 3 naira 500,000.

Bikin kamun kifin Argungu da kuma al’adun gargajiya na janyo daruruwan mutane daga ciki da wajen Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI