"Najeriya na nazarin rage farashin litar mai"
Karamin ministan man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya ce yanzu haka masu ruwa da tsaki na ganawa kan yiwuwar rage farashin litar man fetur a kasar, la’akari da yadda farashin gangar danyen a kasuwar duniya ya koma dala 34 daga dala 53.
Wallafawa ranar:
Sylva ya ce raguwar farashin danyen man ya sanya raguwar kudaden da gwamnati ke kashewa wajen shigar da tattacen man cikin Najeriya.
a baya bayan nan ne dai wani rahoton hukumar kayyade farashin man fetur din a Najeriya ya ce zuwa ranar 10 ga watan Maris da muke ciki, farashin sauke kowace litar tataccen man a kasar na kan naira 95, abinda ke nufin farashin man kan kowace litar da jama’a za su rika saya ka iya komawa naira 114 da kobo 53 bisa hasashe, la’akari da saukin da aka samu a baya.
Takaddama tsakanin Saudi Arabia da Rasha ta sa Saudi da kawayen ta kara yawan man da suke fitarwa zuwa kasuwannin duniya, abinda ya sa farashin faduwa daga Dala 53 kowacce ganga zuwa Dala 33.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu