Najeriya

Jami'an tsaro sun yi katsalandan a zaben 2019 - Amurka

Daya daga cikin rumfunan kada kuri'a a jihar Adamawa yayin zabukan 2019 a Najeriya.  23/2/2019.
Daya daga cikin rumfunan kada kuri'a a jihar Adamawa yayin zabukan 2019 a Najeriya. 23/2/2019. REUTERS/Nyancho NwaNri

Amurka ta ce ta samu hujjojin dake tabbatar dacewa jami’an tsaron Najeriya da suka hada dasojoji da ‘yan sandan DSS sun yiwa masu kada kuri’a, jami’an zabe har ma da masu sa’ido katsalandan ko kuma cin zarafinsu yayin zabukan shekarar 2019.

Talla

Ikirarin Amurkan na kunshe cikin wani rahoto da ma’aikatar cikin gidan kasar ta wallafa, wanda ta gudanar da bincike kan batun kare hakkin dan adam a Najeriya.

Cikin rahoton Amurka ta kara dacewa, har yanzu sashin shari’ar Najeriya na fuskantar barazana yi masa katsalandan daga bangaren zartaswa da kuma ‘yan majalisa, sai kuma matsalar cin hancin da yayiwa sashin shari’ar katutu, abinda ya sanya shi gaza gudanar da ayyukansa cikin ‘yan ci.

Rahoton mai shafuka a akalla 44, ya kuma ce tashe-tashen hankula da matsalolin tsaro sun taka rawa wajen hana jama’a da dama fita kada kuri’unsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI