Najeriya

Tinubu ya bayyana goyon bayansa ga Adams Oshiomhole

Shugaban Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshoimhole daga bangaren hagu, tare da jagoran jam'iyyar ta APC Bola Tinubu.
Shugaban Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshoimhole daga bangaren hagu, tare da jagoran jam'iyyar ta APC Bola Tinubu. PM News Nigeria

Jagoran Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana goyan bayan sa ga Adams Oshiomhole a matsayin shugaban Jam’iyyar ta su, yayin da ya zargi masu bukatar yin takarar zaben shugaban kasa shekarar 2023 a matsayin masu haddasa rigima a cikin jam’iyyar.

Talla

Sanarwar da Tinubu ya sanyawa hannu tace bisa dukkan alamu rikicin da Jam’iyyar ke fuskanta yanzu haka zai bada damar daukar matsayi kan zaben shekara ta 2023 tun kafin mu fice daga wannan shekara ta 2020.

Jagoran ya bayyana Oshiomhole a matsayin jajircacce wajen yakin neman zabe da kuma tara jama’a wa Jam’iyyar APC da ya dace a goyi bayan sa.

Tinubu yace wannan ne dalilin da ya sa ya zama wajibi a goyi bayan shugaban Jam’iyyar duk da yake shima ‘dan Adama ne mai yin kuskure.

Jagoran Jam’iyyar yayi watsi da kiran taron shugabannin Jam’iyyar na kasa da Mataimakin sakataren Jam’iyyar na kasa Victor Gaidom ya kira ranar 17 ga wannan wata domin tattauna matsalar da ta taso, inda yake cewa matakin ba zai taimaki manufofin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.