Najeriya na son hana balaguro saboda Coronavirus
Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen da Coronavirus ta yi kamari, a daidai lokacin cutar ta laukme rayuka fiye da dubu 7 a sassan duniya.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dattawan ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa karin cibiyoyin gwajin cutar, tana mai cewa, guda biyar da ake da su a yanzu, sun yi kadan idan aka kwatanta da yawan al’ummar Najeriya da ya zarce miliyan 200.
Babu ire-iren wadannan cibiyoyin gwaje-gwaje a yankunan kudu maso gabashi da kuma arewacin kasar, abin da ya sa Majalisar ta bukaci samar da cibiyoyin a wadannan wurare.
Kasashen da cutar ta fi kamari sun hada da China da Italiya da Birtaniya da Iran, sai kuma wasu sassan na Turai.
A makon jiya ne, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana nahiyar Turai a matsayin sabuwar cibiyar annubar Coronavirus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu