Najeriya
Najeriya ta soke bikin wasanni na kasa saboda Coronavirus
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Tarayar Najeriya ta dage bikin wasanni na kasa da aka shirya gudanarwa a jihar Edo a bana sakamakon cutar Coronavirus
Talla
Ministan Wasanni da Matasa na kasar, Sunday Dare ya sanar da wannan mataki a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Talata.
A cewar Ministan, daukar matakin na zuwa bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari game da yaduwar annubar.
Kawo yanzu ba a sanar da ranar gudanar da bikin wasannin ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu