Bankin Najeriya ya bayyana shirinsa na tunkarar Coronavirus
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Babban Bankin Najeriya CBN, ya sanar da wasu sabbin matakai don kare tattalin arzikin kasar daga illolin cutar Coronavirus.
Wasu daga cikin matakan sun hada da jinkirta biyan basussukan da ake bin masu kananan masana’antu har tsawon shekara daya, sai kuma rage kudin ruwa daga kashi 9 zuwa 5 cikin dari.
Babban bankin Najeriya ya kuma bayyana shirin ware naira biliyan 50 domin tallafawa iyalai, kanana da matsakaitan masana’antu da tasirin annobar murar coronavirus ya shafa.
Tuni dai masana tattalin arziki suka soma tofa albarkacin bakinsu kan matakai, ko shirin babban bankin Najeriya, musamman kan batun makudan kudaden da zai ware domin bayar da tallafi, la’akari da cewar tattalin arzikin kasar ya tabu, saboda faduwar farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya daga dala 53 zuwa 28 kan kowace ganga.
Wasu daga cikin masanan sun bayyana shakkun nasarar bada tallafin ganin yadda Najeriyar ta dogara ne kan danyen man wajen samun kudaden shiga, yayinda wasu ke ganin idan aka sanyawa shirin idanu hakan zai wadatar.
Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI Kasimu Garba Kurfi, masani tattalin arziki dake birnin Lagos ya goyi bayan batun na sa idanu, wanda ya bukaci maida hankali kan bankuna a kasar ta Najeriya.
Dakta Kasim Kurfi kan shirin Bankin Najeriya na tunkarar Coronavirus
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu