Majalisar Dattawa ta bukaci Buhari ya yi jawabi kan coronovirus

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yiwa al’ummar kasar jawabi kan irin matakan da ake dauka wajen yaki da cutar coronavirus wadda yanzu haka aka tabbatar da cewar mutane 8 sun kamu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. oodweynemedia
Talla

Majalisar ta kuma bukaci daukar kwararan matakai wajen tinkarar matsalar da suka hada da hana baki daga duk kasashen da aka samu cutar da tabbatar da rufe iyakoki da kuam binciken matafiya dake zuwa Najeriya.

Majalisar ta bukaci gwamnati ta rufe daukacin tashoshin jiragen saman kasar banda na Lagos da Abuja, kana da killace duk bakin da suka shiga kasar daga kasashen da aka samu masu dauke da cutar 1,000.

A karshe majalisar ta bukaci ware wasu kudade na musamman domin tinkarar matsalar cutar wadda ta shafi bangarori da dama.

Tuni gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da ziyarar baki daga kasashe 13 da cutar tafi illa cikin su harda China da Amurka da Birtaniya da Italia da Spain da Koriya ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI