Majalisar wakilan Najeriya ta haramta tarukan ibada

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da bukatar haramta gudanar da taron ibada a fadin kasar sakamakon barazanar cutar coronavirus.

Majalisar dokokin Najeriya
Majalisar dokokin Najeriya Reuters
Talla

Majalisar tace ta dauki matakin ne, la'akari da cewa kasashen Saudi Arabia da Iran da kuma Fadar Vatican duk sun dauki irin wannan mataki,  a matsayin matakan kare jama’a na kamuwa daga cutar.

Majalisar ta kuma kafa dokar hana baki ziyarar ofisoshin ta har sai illa masha Allahu.

A karkashin wannan doka, duk wanda ke bukatar ziyarar dan majalisar da ya fito daga mazabar sa, sai ya rubuta masa wasika ya kuma samu amsa kafin ya ziyarci Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI