Najeriya-Coronavirus

Mutane 5 sun kamu da cutar Coronavirus a Najeriya

Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus.
Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus. Getty Images

Ministan Lafiyar Najeriya Osagie Ehanire yace adadin wadanda suka kamu da cutar murar Coronavirus a kasar ya kai mutane 5.

Talla

Ministan ya ce dukkanin mutanen da suka kamu da cutar sun yi tattaki zuwa ko dai Birtaniya ko kuma Ingila.

Rahoton ma’aikatar lafiyar Najeriya ya zo ne jim kadan bayan da gwamnatin kasar ta sanar da haramta zirga-zirga tsakaninta da kasashe 13, ciki har da Birtaniya da Amurka da China da kuma Italiya.

A wani labarin kuma mai alaka da wannan hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ta Najeriya NYSC, ta rufe baki dayan sansanoninta dake sassan kasar saboda rigakafin barkewar annobar Coronavirus.

A baya bayan nan ne kuma ma’aikatar lafiyar Katsina ta bayyana gano mutum na farko a jihar da ya kamu da cutar murar Coronavirus da ta zamewa duniya annoba, bayan bulla a kasashe akalla sama da 145.

Yayin ganawa da manema labarai babban sakataren ma’aikatar lafiyar ta Katsina dakta Kabir Mustafa, ya ce mara lafiyar ya dawo ne daga kasar Malyasia, kuma yanzu haka ya killace kansa da kansa.

Dakta Mustafa ya kara da cewa tuni suka soma kokarin gano wadanda mara lafiyar yayi mu’amala da su lokacin da ya koma gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.