Coronavirus

Najeriya ta bukaci 'yan kasar da su kauracewa taruka

Wani taron Siyasa da ya gudana a garin Lafiya na Jihar Nasarawa dake Najeriya. 1/10/2019.
Wani taron Siyasa da ya gudana a garin Lafiya na Jihar Nasarawa dake Najeriya. 1/10/2019. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Gwamnatin Najeriya ta bada shawarar kauracewa taron jama’a da kuma addinai domin dakile yaduwar cutar coronavirus dake cigaba da kutsawa zuwa sassan duniya.

Talla

Ministan kasa a ma’aikatar lafiyar Najeriya Adeleke Mamora ya bayyana haka, bayanda gwamnati ta sanar da dakatar da bikin gasar wasanni ta kasa da aka shirya farawa a karshen wannan mako.

Yayin jawabin da ya gabatar, ministan yayi gargadin akalla kashi 80 zuwa 81 na mutane na iya kasa nuna alamun cutar, ko kuma idan sun nuna alamar, sai kaga bashi da girma sosai, abinda ke zama babbar hanyar yada cutar cikin al’umma.

Dangane da annobar ta coronavirus, mai yiwuwa a dage wasannin gasar kwallon kafar Najeriya na Premier League saboda matakan samun kariya.

Yau laraba dai ake sa ran sanin makomar babbar gasar kwallon kafar bayan taron masu ruwa da tsakin da hukumar shirya gasar ta kasa wato League Management Company zata jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.