Coronavirus

Najeriya ta haramta zirga-zirga tsakaninta da kasashe 13

Filin jiragen saman Najeriya na kasa da kasa na Murtala Mohammed dake birnin Legas.
Filin jiragen saman Najeriya na kasa da kasa na Murtala Mohammed dake birnin Legas. REUTERS/Akintunde Akinleye/File Photo

Gwamnatin Najeriya ta haramta zirga zirga tsakanin ta da kasashe 13 da cutar coronavirus ta yiwa illa domin kare al’ummar kasarta.

Talla

Sakataren Gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ya sanar da daukar matakin yayin jawabi ga manema labarai kan irin matakan da suke dauka na dakile cutar.

Mustapha ya bayyana kasashen da umurnin ya shafa da suka hada da China da Amurka da Birtaniya da Japan da Iran da Koriya ta kudu da Switzerland.

Sauran sun hada da Norway da Netherlands da Italia da Faransa da Jamus da Spain.

Biyu daga ciin masu dauke da cutar da aka samu sun fito ne daga Italia da Birtaniya, yayin da na 3 kuma ya kamu da ita sakamakon mu’amala da ‘dan kasar Italian.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.