Coronavirus-Najeriya

Gwajin likitoci ya tabbatar da babu Coronavirus a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina dake Najeriya tace gwajin da aka yiwa wani malami da ya ziyarci Malaysia dangane da cutar coronavirus ya nuna cewar baya dauke da cutar.

Coronavirus ta bulla a arewacin Najeriya
Coronavirus ta bulla a arewacin Najeriya Daily Trsut
Talla

A ranar laraba ne dai yayin ganawa da manema labarai sakataren din-din-din na ma’aikatar lafiyar jihar ta Katsina Dr. Kabir Mustapha ya bayyana killace mutumin da ake kyautata zaton yana dauke da cutar bayan dawowarsa daga Malaysia.

Rahotanni sun ce, mutumin ya koma gida ne ranar 9 ga watan Maris, yayin da ya ziyarci danginsa a Karamar Hukumar Safana kafin ya kai kansa asibitin Jami’ar Dutsin-ma dauke da alamomin cutar.

Sai dai bayan kammala gudanar da gwaje-gwaje masu zurfi kan mara lafiyar a Abuja Kwamishinan lafiyar Jihar Katsina Yakubu Nuhu Danja ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewar, sakamakon dake hannunsu ya tabbatar da cewa alamun rashin lafiyar da ma'aikacin yaji bayan dawowa daga Malaysia ba na cutar murar Coronavirus bane.

Kwamishinan ya kuma bukaci jama'a da su kaucewa yada larabarai marasa tushe ta kafafen sadarwa na zamani don jefa mutane cikin rudani.

Kwamishinan lafiyar Jihar Katsina Yakubu Nuhu Danja

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI