Najeriya

Farashin man fetir ya koma Naira 125 a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wajen hakar man fetir
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wajen hakar man fetir Vanguard Nigeria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni rage farashin man fetur daga Naira 145 zuwa naira 125 a kan kowace lita.

Talla

Daukar matakin ya biyo bayan wata ganawa ce da aka yi tsakanin shugaban kasar da kuma karamin ministan albarkatun mai Timipre Sylva a taron majalisar koli ta kasar a jiya laraba.

Daukar matakin na da nasaba da cutar Coronavirus da ta kasance ummul-haba’isin tabarbarewar farashin man fetir a kasuwannin duniya, inda ganga guda ta koma Dala 30 daga Dala 60

Karaminin Ministan ya ce, shugaba Buhari ya rage farashin man ne don ‘yan Najeriya su amfana daga tabarbarewar farashin a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.