Karin mutane 4 sun kamu da Coronavirus a Najeriya
Hukumomin Najeriya sun ce an sake samun karin wasu mutane 4 dake dauke da cutar coronavirus abinda ya kawo adadin mutanen da suka kamu a kasar zuwa 12.
Wallafawa ranar:
Kwamishinan lafiyar Jihar Lagos Akin Abayomi yace mutanen 4 da suka shiga Najeriya daga Jamus a karshen mako na daga cikin mutane 19 da aka yiwa gwaji.
Abayomi yace wadannan mutanen sun sauka a Lagos ne daga jirgin Luftansa da ya fito daga Frankfurt, kuma yanzu haka suna farautar mutane sama da 1,300 da ake zargin sun yi mu’amala da amsu dauke da cutar.
Ya zuwa yanzu mutane 12 aka tabbatar suna dauke da cutar a Najeriya, kuma babu wanda ya rasa rai.
Ko a jiya sanda aka gano mutane 5 da suka kamu da cutar daga cikin wadanda suka shiga Najeriya daga Birtaniya da Amurka.
Najeriya ta dakatar da zirga zirgar jiragen sama daga kasashe 13 da cutar ta yiwa illa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu