Najeriya-Coronavirus

'Yar Buhari ta killace kanta bayan komawa Najeriya daga Turai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Uwargidansa Aisha Buhari, da 'ya'yansu da kuma sauran 'yan uwa a fadar gwamnati dake Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Uwargidansa Aisha Buhari, da 'ya'yansu da kuma sauran 'yan uwa a fadar gwamnati dake Abuja. Photo credit: Twitter / @MBuhari

Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta sanar da cewar an killace daya daga cikin ‘yayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta koma kasar daga Birtaniya saboda kaucewa kamuwa da cutar coronavirus.

Talla

Aisha Buhari ta sanar da haka ne a sakon twitter da ta aike, inda take cewar ‘yar ta su bata nuna aalamun kamuwa da cutar ba, sai dai sun dauki matakin ne sakamakon shawarar da kwamitin yaki da cutar ya ba su.

Uwargidan shugaban tace ta yanzu haka ta rufe ofishin ta na makwanni biyu inda ta bukaci ma’aikatan ta su dinga aiki daga gidajen su, yayin da ta yabawa gwamnonin arewa maso yamma da suka rufe makarantu domin kare dalibai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI