Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe makarantun kasar
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe baki dayan makarantun kasar manya da kanana a matsayin matakin dakile yaduwar annobar murar Coronavirus da ta bulla a kasar.
Yau juma’a ake sa ran Ministan ilimin Najeriya ya sanar da lokacin soma aikin umarnin rufe makarantun da kuma tsawon wa’adin da za su kasance a rufe.
Sai dai sanarwar da Ministan ilimin najeriya Adamu Damu ya fitar, ta bukaci gaggauta kammala zangon karatu na 2 a baki dayan makarantun sakandaren tarayyar Najeriya ciki har da zana jarrabawa, kafin ranar 26 ga watan maris da muke ciki.
Yanzu haka dai alkalumman hukumomin lafiya na duniya sun tabbatar da bullar annobar murar Coronavirus a kasashe da manyan yankuna 157.
Zalika annobar da ta lakume rayuka kusan dubu 10, ta tilastawa daliban manya da kananan makarantu sama da miliyan 800 a sassan duniya zaman gida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu