Coronavirus

An killace masu Coronavirus a jihar Nasarawa

Cutar Coronavirus ta lakume rayuka fiye da dubu 10 a sassan duniya
Cutar Coronavirus ta lakume rayuka fiye da dubu 10 a sassan duniya AFP / Joseph Prezioso

Gwamnatin jihar Nasarawa da ke Najeriya ta sanar da killace wasu mutane 5 'yan gida guda a asibitin Keffi bayan zargin cewa, sun harbu da cutar Coronavirus.

Talla

Kwamishinan Lafiyar Jihar Ahmed Yahya ya bayyana haka inda ya ce, mutanen sun fito ne daga Jihar Ogun zuwa garin Keffi, kuma sun nuna alamun kamuwa da cutar.

Yahya ya ce, tuni aka dauki samfurin jinin mutanen aka kuma aika da shi zuwa Cibiyar Yaki da Cututtuka da ke birnin Abuja domin gudanar da bincike a kai.

Kwamishinan ya ce, za a ci gaba da killace iyalan har zuwa lokacin da za a samu sakamakon gwajin.

Jihar Nasarawa na daya daga cikin jihohin da suka sanar da rufe makarantun gwamnati a matsayin riga-kafin kamuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.