Likitocin Najeriya na yajin aiki a yayin da Coronavirus ke barna
Kungiyar Likitocin Najeriya ta bai wa ‘yayanta da ke yajin aiki a wasu jihohin kasar da su gaggauta komawa bakin aiki domin taimaka wa gwamnati wajen dakile yaduwar cutar Coronavirus.
Wallafawa ranar:
Shugaban Kungiyar Francis Faduyile ya bayyana haka a birnin Abuja, inda ya ce, shugabannin kungiyar na kasa za su karbe tattaunawa da rassan kungiyoyin da ake takun-saka domin warware matsalar.
Faduyile ya bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta samar da isassun kayan aiki ga ma’aikatan lafiyar da ke fuskantar wannan matsala ta kula da masu dauke da cutar.
Kungiyar ta kuma bukaci samar da wurare masu kyau da za a rika killace wadanda aka gano dauke da cutar.
Ya zuwa yanzu Kungiyar Likitocin rassan Abuja da Gombe da Enugu da Kaduna da kuma Cross Rivers ke yajin aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu