Najeriya ta bada umarnin rufe filayen jiragen samanta guda 3
Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe filayen jiragen samanta na kasa da kasa guda 3 a wani yunkuri na cigaba da daukar matakan dakile yaduwar annobar Coronavirus a kasar.
Wallafawa ranar:
Filayen jiragen saman da za a rufe sun hada da na Malam Aminu Kano dake Kano, filin jiragen sama na Omagwa dake Fatakwal, da kuma filin jragen sama na kasa da kasa na Akanu Ibiam dake Enugu.
Umarnin rufe filayen jiragen saman sai soma aiki daga 21 ga watan Maris da muke ciki.
Sai dai Filayen jiragen saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da na Murtala Muhammad dake Legas za su kasance a bude, amma ba za a kyale saukar duk wani jirgi da ya taso daga cikin kasashe 13 da Najeriya ta haramta zirga zirga tsakaninta da su.
Kasashen da Najeriya ta sanyawa takunkumin zirga-zirgar sun hada da Amurka, Birtaniya, China, Faransa, Italiya, Spain da kuma Jamus.
Sauran su ne Japan, Norway, Switzerland, Iran, Netherland da kuma Korea ta Kudu.
Rahotanni a baya bayan nan kuma sun ce Najeriyar ta sanya kasashen Austria da Sweden cikin kasashen da ta kakabawa takunkumin zirga-zirgar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu