Najeriya

Tsokacin Trump ya kwantar da 'yan Najeriya a asibiti

'Yan Najeriya sun kamu da rashin lafiya bayan kwankwadar maganin Kulorokwin
'Yan Najeriya sun kamu da rashin lafiya bayan kwankwadar maganin Kulorokwin devex

Hukumomin Najeriya sun ce, an samu mutanen da suka kamu da rashin lafiya sakamakon kwankwadar maganin Kulorokwin bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ce, za su samar wa Amurkawa da maganin domin magance cutar Coronavirus.

Talla

Ore Awokoya, babbar mai taimaka wa gwamnan Jihar Lagos ta ce, asibitocin da ke birnin sun gabatar da rahotan mutanen da suka kamu da rashin lafiya sakamakon kwankwadar wannan magani bayan da shugaban Amurka ya yi magana a kan sa.

Jami’ar ta bayyana damuwa kan yadda mutane suka yi gaban kansu wajen kwankwadar wannan magani ba tare da barin masana kiwon lafiya ko kuma Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi bayani a kai ba.

Awokoya ta ce, yanzu haka ana kula da biyu daga cikin ire-iren wadannan mutane, kuma suna sa ran samun fiye da haka a kwanaki masu zuwa.

A ranar Alhamis ne shugaba Trump ya ce, Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta amince a yi amfani da Kulorokwin wanda ya yi suna wajen magance zazzabin cizon sauro.

Shugaban na Amurka ya ce, za su samar wa Amurka maganin cikin 'yan kwanaki masu zuwa saboda yadda a ka yi amfani da shi a China da Faransa kuma a ka samu nasara.

Daga bisani shugaban Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Amurka ya ce, basu kammala bada damar amfani da maganin ba tukunna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.