Najeriya-Dubai

Manyan 'yan siyasar Najeriya sun mallaki kadarori 800 a Dubai

Wani sashi na Dubaï, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa.
Wani sashi na Dubaï, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa. REUTERS/Karim Sahib

Wani binciken da aka gudanar ya nuna cewar manyan Yan siyasar Najeriya na daga cikin mutanen da suka mallaki manya manyan gidaje da shaguna da kuma dakunan otel otel a Dubai dake kasar Daular Larabawa.

Talla

Binciken ya bayyana cewar daga cikin manyan kadarori 800 da suka mamaye birnin Dubai da akayi yiwa kudi akan naira biliyan 164, akwai Yan Najeriya 334 da sunayen su ya bayyana cewar su suka mallake su da kudaden da aka bayyana cewar an same su ne ta hanyar da bata kamata ba.

Binciken da Cibiyar Carnegie dake Amurka ta gudanar wanda aka wallafa da Mathew Page ya jagoran ta ya bayyana wasu daga cikin ‘yan Najeriyar dake da kadarorin a Dubai da suka hada da Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu da tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da Alh Nasir Mantu da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP Ahmadu Ali da tsohuwar shugabar bankin Oceanic Cecilia Ibru.

Rahotan yace akwai sunayen tsoffin Gwamnoni 20 da masu ci 15 da Yan Majalisu 16 da ministoci 15 da ma’aikatan fadar shugaban kasa 5 da alkali guda da jami’an kamfanin man NNPC 5 da manyan hafsoshin tsaro 13.

Binciken yace Daular Larabawa ta zama wani babban dandalin boye dukiyar sata da Yan siyasa da kuma Yan kasuwar duniya ke kwashewa daga kasashen su inda sue zuwa su sayi kadarori domin batar da kudaden.

Alakar shugabannin kasar da kuma manyan kasashen duniya irin na matukar tarnaki wajen kwashe irin wadannan kudaden domin mayar da su kasashen da ak asato su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.