Coronavirus

Najeriya ta sanar da karin mutune 10 da suka kamu cutar Coronavirus

Hoton zubin kwayar cutar Coronavirus da ta zamewa duniya annoba.
Hoton zubin kwayar cutar Coronavirus da ta zamewa duniya annoba. (Photo By BSIP/UIG Via Getty Images)

Gwamnatin Najeriya tace an sake samun mutane 10 da suka kamu da cutar coronavirus, abinda ya kawo adadin mutanen da suka kamu a kasar zuwa 22.

Talla

Cibiyar yaki da cututtuka ta sanar da cewar daga cikin sabbin mutane 10 da suka kamu da cutar, 7 na Lagos ne, yayin da guda 3 kuma ke zama a Abuja.

Cibiyar tace 9 daga cikin masu dauke da cutar sun dawo ne daga tafiya zuwa kasashen waje, yayin da guda daga cikin su kuma ya samu cutar wajen mu’amala da wadanda ke dauke da ita.

Sanarwar tace duk sabbin kamun sun nuna alamun farko na kamuwa da cutar kuma ana kula da su a asibitin koyarwar Jami’ar Abuja da asibitin yaki da cututtuka dake Lagos.

Tuni dai aka sallami mutane biyu da suka warke, cikin su harda dan kasar Italia da ya fara zuwa da cutar da kuma wanda yayi mu’amala da shi.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci al’ummar kasar da su kwantar da hankalin su wajen bin shawarwarin da aka basu wajen kauceaw kamuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.