Coronavirus-Najeriya

Najeriya za ta tafka hasarar guraben ayyuka dubu 22 - IATA

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta duniya IATA, ta ce takaituwar zirga-zirga saboda annobar Coronavirus dake yaduwa zai haddasawa Najeriya tafka hasarar sama da naira biliyan 160, gami da rasa guraben ayyukan yi akalla dubu 22, da 200 a fannin sufurin jiragen saman kasar.

Cikin harabar filin jiragen saman na Murtala Mohammed dake birnin Legas a Najeriya.
Cikin harabar filin jiragen saman na Murtala Mohammed dake birnin Legas a Najeriya. REUTERS/SCANPIX
Talla

Hukumar sufurin jiragen saman ta duniya, ta kuma kiyasta cewar kamfanonin jiragen saman dake Najeriya za su rasa fasinjojinsu kimanin miliyan 2 da dubu 200, biyo bayan ci gaba da soke tashin jirage zuwa sassan Nahiyar Afrika, bayan da kasashe suka rika daukar matakan garkame iyakokinsu ciki har da na sama, domin dakile yaduwar annobar murar Coronavirus da ke barazana ga duniya.

A karshen makon nan hukumar ta IATA, tace sauran hukumomi da kamfanonin jiragen sama na kasashe na bukatar tallafin akalla dala biliyan 200, domin ceto su daga durkushewa.

IATA ta ce kamfanonin jiragen sama dake nahiyoyin Yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Afrika ne suka fi bukatar tallafin la’akari da mummunan tasirin da annobar murar Coronavirus ta yiwa sufurinsu na jiragen sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI