Najeriya ta haramtawa jirage daga kasashen ketare shiga cikinta
Gwamnatin Najeriya ta rufe filayen jiragen samanta na Murtala Muhd dake Legas da kuma na Nnamdi Azikiwe dake Abuja daga sufurin jiragen sama na kasa da kasa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Cikin sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan hukumar kula da sufurin jiragen saman Najeriya Musa Nuhu, gwamnati ta ce dokar za ta soma aiki daga ranar litinin, sai dai sufurin jiragen saman zai ci gaba da gudana a cikin gida.
A halin da ake ciki Najeriya ta kammala rufe baki dayan filayen jiragenta na kasa da kasa ga jirage daga kasashen ketare saboda annobar murar Coronavirus da a yanzu ta kutsa sama da kasashe 150.
Sa'o'i kadan bayan rufe filayen jiragen da Najeriya ta yi, manyan kamfanonin jiragen sama dake Turai, da Gabas ta Tsakiya da kuma sauran sassan duniya suka sanar da nasu matakin na dakatar da zuwa Najeriya.
Kamfanonin jiragen saman kasashen ketaren da suka dauki matakin kuwa sun hada da Air France, Lufhtansa dake Jamus, Emirates na hadaddiyar Daular Larabawa da kuma KLM na kasar Netherlands.
Yanzu haka dai adadin masu dauke da cutar murar Coronavirus a Najeriya ya kai 22, bayan samun karin mutane 10 da annobar ta shafa daga alhamis din da ta gabata zuwa jiya asabar.
Cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya tace daga cikin sabbin mutane 10 da suka kamu da cutar, 7 na Lagos ne, yayin da guda 3 kuma ke Abuja.
Cibiyar tace 9 daga cikinsu sun dawo ne daga kasashen waje, guda kuma ya samu cutar wajen mu’amala da wadanda ke dauke da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu