Coronavirus

Yawan wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya ya kai 30

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP

Gwamnatin Najeriya tace adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus yak ai 30 a fadin kasar, bayan samun karin mutane 3 da suke dauke da ita a Lagos.

Talla

Ma’aikatar lafiyar Jihar Lagos tace cikin sabbin mutane 3 da aka samu dauke da cutar akwai dan Birtaniya da ya shiga Najeriya ranar 8 ga wata da wani dan Najeriya da ya koma gida daga London sai kuma wani BaAmurke da yaje kasar makwanni 6 da suka gabata.

Yayin jawabi na farko da ya gabatarwa al'ummar kasar, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa daukar matakan da suka dace domin kare lafiyar al’ummar kasar.

Jawabin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan annobar Coronavirus

A wani labarin kuma gwamnatin makwabciyar Najeriya, wato Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da samun mutumi na biyu da ya kamu da cutar coronavirus, bayan wanda aka samu na farko a makon jiya.

Ministan lafiya Dr Ilyasu Idi Mainasara yace wani dan kasar Italia aka gano yana dauke da cutar.

Ministan lafiyar Jamhuriyar Nijar Dakta Ilyasu Idi Mainasara

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI