Najeriya-Coronavirus

Gwajin likitoci ya tabbatar da babu Coronavirus a Kano

Wasu jami'an lafiya da ke kula da masu dauke da cutar Coronavirus.
Wasu jami'an lafiya da ke kula da masu dauke da cutar Coronavirus. Quartz

Wani jirgin sama da ya sauka a birnin Kano dake arewacin Najeriya a safiyar yau, ya haifar da rudani kan yuwuwar bullar cutar corona Virus karon farko a birnin.

Talla

Jirgin wanda aka ce ya taso ne daga jihar Lagos dake kudancin kasar an sami wani yaro na shekara 17 da ya yi amai a cikin jirgin, abinda ya sanya matukin su yaki bari kowa ya fita.

Dr Muhammad Balarabe Abdullahi babban jami’in da ke lura da cibiyar da aka ware don killace masu wannan cuta a jihar ta Kano, ya bayyana cewa gwajin da aka yiwa yaron ya nuna baya dauke da cutar ta corana, hasalima bai yi mu'amala da wani da ake tsammanin yana dauke da cutar ba.

Ko a makon jiya hankulan jama'a ya tashi a makociyar jihar ta Kano wato Katsina bayan da jita-jita ta baza gari kan cewa wani magidanci na dauke da cutar, amma kuma bayan gwaje-gwajen likitoci ya nuna cewa baya dauke da ita.

Kawo yanzu dai Najeriya na da akalla mutane 42 da ke dauke da cutar, inda mutum guda ya mutu a Abuja babban birnin kasar yayinda jihar Lagos ke matsayin mafi yawan masu dauke da cutar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.