Najeriya

Mayakan ISWAP sun halaka dakarun Najeriya 70

Wasu dakarun sojin Najeriya dake yakar mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wasu dakarun sojin Najeriya dake yakar mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar. Reuters

Rahotanni daga Najeriya sun ce mayakan ISWAP sun halaka akalla sojojin kasar 70, a wani mummunan farmaki da suka kai musu ta hanyar kwanton Bauna a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Talla

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wasu jami’ai biyu da suka shaida mishi cewar, mayakan sun farwa dakarun Najeriyar ne da makaman roka, a dai dai lokacin da tawagarsu ke gaf da kauyen Gorji dake jihar Borno.

Daya daga cikin jami’an da suka nemi sakaya sunansu, ya ce anyi nasarar zakulo gawarwakin sojin Najeriyar 70, sai dai akwai fargabar karuwar adadin wadanda suka mutu, la’akari da cewar har zuwa lokacin wallafa labarin aikin ceto na gudana.

Bayanai dai sun ce sojoji da dama sun jikkata yayin farmakin, yayinda mayakan na ISWAP suka yi awon gaba da sauran.

Tawagar sojin dakarun Najeriyar sun taso ne daga garin Maiduguri da nufin kaddamar da gagarumin farmaki kan sansanin mayakan na ISWAP a lokacin da suka fada tarkon kwanton Baunar.

ISWAP dai tsagin kungiyar Boko Haram ne da suka bijirewa jagorancin Abubakar Shekau, wadanda a yanzu ke yiwa kungiyar IS ko ISIS da ta durkushe a yankin gabas ta tsakiya biyayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI