Nigeria

Adadin masu dauke da Coronavirus a Najeriya ya haura 44

Ana gwajin zafin jikin wata mata a asibin soji dake Lagos a Najeriya saboda coronavirus
Ana gwajin zafin jikin wata mata a asibin soji dake Lagos a Najeriya saboda coronavirus AFP / Getty Images

Hukumomin Najeriya sun ce adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a kasar ya tashi zuwa 44, sakamakon gano Karin mutanen da suke dauke da cutar.

Talla

Wannan ya biyo bayan labarin cewar Babban Hafsa a fadar shugaban kasa Abba Kyari da Gwamnan Bauchi Bala Muhammed da kuma wasu mutane biyu, daya a Lagos daya a Ogun na dauke da cutar.

Hukumar yaki da cututtuka a kasar ta ce wasu mutanen biyu sun fito ne daga Lagos da Ogun, kuma daya daga cikin su ya koma kasar ne daga tafiyar da ya yi zuwa kasar waje, yayin da na biyu kuma ya samu cutar ne daga mu’amala da wani mai dauke da ita.

Hukumar ta ce wannan ne karo na farko da aka samu wani da ke dauke da cutar da ya sanyawa wani tun bayan bullar cutar a kasar watan jiya.

Wannan labari ya nuna cewar Lagos ke sahun gaba wajen yawan masu dauke da cutar, sai kuma Abuja  da Ogun da Jihohin Ekiti da Oyo da Edo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.