Mataimakin shugaban Najeriya ya killace kansa

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. Solacebase

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya killace kan sa, yayin da ya cigaba da gudanar da ayyukan sa daga gida kamar yadda hukumar yaki da cututtuka ta bada shawara.

Talla

Kakakin mataimakin shugaban kasar Laolu Akande yace ranar Talata, Osinbajo ya gudanar da tarurrukan sa ta bidiyo domin nesanta kan sa ga jama’a.

Ya zuwa yanzu babu tabbaci kan dalilin da ya sa mataimakin shugaban ya killace kan sa, sai dai rahotanni na cewa wata kila yana da nasaba da rahotannin samun masu dauke da cutar a fadar shugaban kasa.

Yanzu haka shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeiya Abba Kyari ya kamu da cutar coronavirus, bayan gwajin lafiyarsa da cibiyar bincike da dakile yaduwar cutuka ta NCDC tayi.

Sai dai gwaje-gwajen jami'an lafiyar ya nuna cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari baya dauke da cutar kamar yadda akewa duk wanda aka gano makusancinsa na dauke da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI