PDP ta bukaci wani Gwamna da ya yi gwajin coronavirus
Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya, reshen jihar Kogi, ta shawarci Gwamna Yahaya Bello ya ga gaggauta kai kansa don ayi masa gwajin cutar coronavirus, sakamakon hulda da ya yi da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya Abba Kyari.
Wallafawa ranar:
Abba Kyari wanda tuni aka tabbatar da ya kamu da cutar, ya kasance babban jami’in gwamnati da ya halarci sadakar uku na rasuwar mahaifiyar Gwamna Yahaya Bello da akayi makon jiya a garin Okene.
Tun bayan da aka wallafa hutun da Kyari ya yi ta musabaha da Gwamna Bello da mukarrabansa, aka shiga jita-jitar cewar ya killace kansa.
Sai dai kwamishinan lafiyar jihar Dr. Saka Haruna ya karyata cewa gwamnan ya kamu da cutar, inda ya bakaci al’umma da suyi watsi da batun.
Cikin sanarwar da jam’iyyar PDP ta fitar dauke da sahannun daraktan bincike da tara bayanai na jam’iyyar Achadu Dickson, ta ce baza ayi nasarar yaki da cutar Covid – 19 ba, sai har masu ruwa da tsaki sun dauki nauyin da ya rataya a wuyarsu, tare da kira ga daukacin wadanda sukayi alaka da babban hadimin shugaban kasar da suje ayi musu gwajin cutar coronavirus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu