Najeriya-Coronavirus

Za'a rufe kasuwannin Lagas saboda coronavirus

Gwamnatin Jihar Lagos dake Najeriya ta bukaci rufe daukacin kasuwannin da basa sayar da kayayyakin da ake matukar bukatar su domin ceto rayuwar jama’a na kwanaki 7 daga ranar Alhamis.

Kasuwar Balagun a birnin Lagas tarayyar Najeriya
Kasuwar Balagun a birnin Lagas tarayyar Najeriya REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Gwamnan Jihar Babajide Sanwo-Olu ya sanar da haka inda yake cewa umurnin bai shafi kasuwannin sayar da kyayyakin abinci da ruwan sha da magunguna da kayan asibiti da kuma kayayyakin da ake bukata domin rayuwa ba.

Sanwo-Olu ya kuma bukaci rufe gidajen barasa da wuraren shakatawa da wuraren motsa jiki da wuraren ninkaya sakamakon samun karuwar wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Jihar.

Gwamnan yace daukar wannan mataki ya biyo bayan yadda aka samu masu dauke da cutar daga 19 zuwa 29 a cikin kwanaki biyu.

Dangane da gidajen sayar da abinci kuwa, Gwamnan ya basu shawarar sayar da abincin ga jama’a amma ba tare da barin jama’a suna ci a cikin su ba.

Sanwa-Olu ya bukaci kamfanoni masu zaman kan su da su umurci wasu daga cikin ma’aikatan su da su zauna a gida, yayin da ya bukaci takaita tafiye tafiye zuwa Lagos ta jiragen sama ko mota, kana kuma ya bukaci mazauna Lagos da su kaucewa zuwa wasu Jihohi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI