An kafa dokar hana fita a Kaduna saboda coronavirus
Gwamnatin Jihar Kaduna dake Najeriya ta bayyana dokar hana fita daga gidaje a matsayin rigakafin kare Jihar daga samun cutar coronavirus wadda ke cigaba da lakume rayukan jama’a.
Wallafawa ranar:
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Dr. Hadiza Balarabe ta sanar da daukar matakin a jawabin da ta yiwa al’ummar Jihar sakamakon shawarar da kwamiti na musamman da aka kafa ya baiwa gwamnati.
Kwamitin yace sakamakon rashin gamsuwa da yadda jama’ar Jihar basa aiwatar da shawarwarin da aka basu na zama gidajen su da kuma barazanar samun cutar ya zama wajibi gwamnati ta dauki wannan mataki domin kare jama’a.
Dr. Balarabe tace daga daren Alhamis din nan ya zama dole kowa ya zauna a gidan sa, babu zuwa ofis ko wuraren kasuwanci ko zuwa wuraren ibada, sai dai kawai mutanen da ya zama dole su je wurin ayyukan su irin su ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro da makamantan su.
Mataimakiyar Gwamnan tace za’a rufe Masallatai da Mujami’u a fadin Jihar baki daya, yayin da za’a bar matafiya zuwa wasu Jihohi su ratsa jihar ta hanyar bayan gari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu