Mutane 6 sun warke daga coronavirus a Najeriya

Gwamnatin Jihar Lagos dake Najeriya ta bayyana shirin sallamar Karin mutane 6 da suka warke daga cutar coronavirus ko kuma COVID-19.

Yadda wasu ma'aikata a Najeriya ke daukan matakan kariya da cutar coronavirus a ma'aikatarsu
Yadda wasu ma'aikata a Najeriya ke daukan matakan kariya da cutar coronavirus a ma'aikatarsu REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Tunde Ajayi, mai taimakawa Gwamnan Jihar Lagos a bangaren kula da lafiya ya bayyana haka a sakon da ya aike ta kafar twitter yau alhamis.

Ajayi yace 6 daga cikin mutane 31 da ake kula da su a Lagos sun warke kuma nan bada dadewa ba za’a sallame su domin su koma gidajen su.

Wannan ya kawo adadin mutanen da suka warke daga cutar a Najeriya zuwa 8, bayan mutane biyu da aka sallama cikin su harda ‘dan kasar Italia da aka fara samun yana dauke da cutar.

Jihar Lagos ke sahun gaba wajen samun masu dauke da cutar kamar yadda hukumar yaki da cututtuka ta Najeriya ta sanar cewar ta samu mutane 31, sai kuma Abuja mai mutane 10, kana kuma Jihar Ogun na da mutane 3, sai Jihohin Oyo da Edo da Bauchi da Osun da Rivers masu mutuum guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI