Najeriya-Coronavirus

Adadin masu dauke da coronavirus a Najeriya ya kai 70

Adadin ‘yan Najeriya da suka kamu da cutar coronavirus ya tashi zuwa 70 tun bayan gano mutumi na farko da ya kamu da cutar a watan jiya.

Matakan kulle hanci don kariya daga coronavirus.
Matakan kulle hanci don kariya daga coronavirus. AFP / Pius Utomi Ekpei
Talla

Alkaluman da hukumar yaki da cututtuka a Najeriya ta bayar sun ce an samu karin mutane 5 da suka kamu da cutar, abinda ya kawo adadin wadanda suka kamu daga 65 a jiya alhamis zuwa 70 yanzu haka.

Hukumar yaki da cututtukan tace an samu sabbin mutane 3 da suka kamu da cutar a Abuja, yayin da aka samu mutane 2 a Jihar Oyo.

Wannan ya nuna cewar har yanzu Lagos ke dauke da mutane 44 sai Abuja mai 14 sai Ogun da Oyo masu mutane uku-uku sai Bauchi mai mutane 2 kana Jihohin Ekiti da Edo da Osun da Rivers ke da mutum guda guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI