Najeriya-Coronavirus

Buhari zai baiwa NCDC naira biliyan 5 don yakar COVID-19

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFI Hausa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin mikawa cibiyar yaki da cututtuka NCDC naira biliyan 5 don samar da isassun kayan aiki dan tinkarar yaki da cutar coronavirus ko kuma COVID-19.Buhari ya kuma amince da bai wa Cibiyar jiragen saman fadar shugaban kasa domin gudanar da ayyukan su idan bukatar hakan ta taso.

Talla

Sanarwar da fadar shugaban kasar Najeriya ta gabatar ta ce shugaba Buhari ya amince da bai wa gwamnatin Jihar lagos naira biliyan 10 a matsayin tallafi domin yaki da cutar a matsayin ta na jihar da tafi samun masu dauke da ita.

Buhari ya kuma amince da bukatar kwaso kwararrun likitocin Najeriya da ke Congo Brazzaville wajen samun horo a wajen Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya domin ba da gudumawa a gida.

Shugaban kasar ya kuma bada umurnin kara yawan kayan gwaji da na aikin likitoci da kuma yawan wuraren gwajin da kuma kiran jami’an kiwon lafiya da suka yi ritaya domin bada gudunmawar su.

Gwamnatin Najeriya ta kuma sanar da rufe iyakokin kasar na makwanni 4 da hana jiragen sama daga kasashen duniya tashi da sauka a kasar da kuma mayar da sansanin tashin alhazai a matsayin inda za a killace wadanda suka kamu da cutar a Abuja.

Haka zalika shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan kasar da su mutunta umarnin da masana kiwon lafiya da kuma gwamnati ke basu domin kaucewa kamuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI